<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>441</hymn_number>
<title>Kasa Kunne Ga Gargaɗin Allah LW441</title>
<lyrics>[V1]
 KORUS
 Kasa kunne ga gargaɗin Allah yana gargaɗin masu bi
 Kada ku yi tarayya fa tare da marasa bangaskiya
 Ku fito daga cikinsu ku ware fa in ji Yesu
 (Mutum 1 : &quot;Kada ku&quot;) taɓa kowane abu marar tsarki in karɓe ku
 (Mutum 1 : &quot;Ku zo ku&quot;)

[V2]
 1) Zama yaya maza da mata gareni
 In ji Ubangiji shi mai iko duka
 Ina gamin haikalin Allah da gumaka
 Ina rabon mai bada gaskiya kuma ?
 Wurin mara bada gaskiya in ji Yesu Mai Ceton duniya
 (Solo : &quot;Idan fa&quot;) mutum yana cikin Almasihu Yesu
 Tsofoffin ayyuka duka sun shuɗe fa
 Sun zama sabobbi cikin Yesu.
 Korus

[V3]
 2) Ayyukanmu a bayyane a wurin Allah mai iko duka
 Fasakanci da kazamata Allah ba ya jin daɗin irinsu
 Tsatsaguwa, kishi kishi, magabtaka da husuma
 (Solo: &quot;Irin su&quot;)
 Ba za su shiga mulkin Allah Ubangijinmu ba
 (Solo: &quot;Don haka&quot;)
 Korus

[V4]
 3) Ekklesiyar Almasihu mu bar aikata zunubi fa
 Domin Allah Ubangiji sarkin saka ba ya kusantuwa
 Shi wanda zakin idonsa ba ya kallon shirinka
 (Solo: &quot;Abinda&quot;) Allah ba ya so shi ne zunuban da mu ke yi
 (Solo : &quot;Lallai ne&quot;)
 Korus</lyrics>
</song>